Brighter Brains

Education, Humanism, Sustainability, Women's Equality

Home > Articles > Mubarak Bala Translates Amsterdam Declaration 2002 for Humanism - into Hausa/Fulani

Mubarak Bala Translates Amsterdam Declaration 2002 for Humanism - into Hausa/Fulani

Posted: Fri, July 21, 2017 | By: HumanismMubarak Bala - a leader of Nigerian humanism and a Brighter Brains Institute advisor - recently translated the Amsterdam Declaration 2002 for Humanism into Hausa/Fulani.

Following a successful humanism congress in Lagos, Nigeria a week ago, which gathered delegates from nations across Africa and the U.K., the suggestion was raised to translate the Amsterdam Declaration into more African Languages, due to interest from people across the continent who are moving away from superstition.

Mubarak Bala
Mubarak Bala

Bala responded by translating the declaration into Hausa/Fulani, a language used by about a 100m people in West Africa, from Senegal and Mali to Sudan and south as far as Gabon.

He was assisted by Abu Manzo and Abdul Razi, his humanist elders from the region.

Below is his translation:

“Kaifin tunani, fadadadde shi ya haifar da falsafa, wadda ita kuma ta haifi kimiyya da fasaha.

Tubalan ginin Insaniyya ta wannan zamani dai sun hada da:

1. Insaniyya tana tafiya ne bisa tarbiyya da kirki. Tana jaddada ‘yanci, daraja, da kima ta duk wani mutum.

Dukkan wani ‘yanci wanda bai shiga ko cutar da wani ba, to ya fado cikin hakkokin jama’a, wanda kowa ya kamata ya iya samunsa, ba tare da tsangwama ko cin zarafi ba.

Masu bin akida ta Insaniyya, sun daukarwa kansu nauyin kula da damuwar duk sauran jama’a, da ma wadanda ba’a haifa ba masu zuwa a nan gaba.

Masu bin Insaniyya, sun yarda cewa ita tarbiyya da kishin ci gaban danAdam, ginannen abu ne a halittar kowa. Bisa fahimtar juna, damuwa da damuwar wasu, kuma suna yin hakan ne ba tare da an tilasta musu ba.

Su masu Insaniyya, sun yarda cewa warware matsalolin al’umma, da matsalolin rayuwa, ya ta’allaka ne da tunani da kuma aiki da fikira, ba wai dogaro da tatsuniyoyi, chamfi ko addu’o’i ga wasu alloli ba.

2. Insaniyya na dogaro ne da kimiyya da kere-kere da dabaru na ilmi, da tambayoyi hadi da bincike wajen nemo hanyoyin warware kowacce irin mas’ala cikin hikima da wasa kwakwalwa, ba wai chamfe-chamfe na addinai ba.

Insaniyya ta karfafa a mahangar kimiyya da fasaha wajen nemo alheri ba sharri ba, ba kuma barna da halaka ba. Kimiyya na iya zama hanya kenan wadda ka iya doras da zama lafiyar bil-adama, hakan kuma dama, shine yafi komai a’ala.

3. Insaniyya na tafiya ne da dimokuradiyya da ma ‘yancin Dan-Adam. Tana zumudin ciyar da dukkan Dan-Adam gaba. A wannan rayuwa, dimokuradiyya, da ‘yanci kowa ya kamata ya zamana yana iya cin moriyar su.

Dimokuradiyya kuma ba wai ta tsaya bane a gwamnatance kadai, a’a, har ma a sauran zamantakewa, walau a kungiyance, a siyasance, a makwabtaka da ma dukkan wata sabga da rayuwar yau da kullum.

4. Insaniyya dai tana bukatar hade sanin yanci ga kowa, da kuma kyautata wa juna. Fahimtar zamani ce, cewa dukkan mu mun dogara ne da duniyar da muke ciki, mun kuma dogara da arzikinta ne, wannan ya saka dole mu kyautata muhalli, wato mu cancana arzikin ita kanta duniyar.

Insaniyya bata tilasta kowa ba, bata kuma da addini. Ilimi dai ta saka a gaba, sanin shi, bincike, fadada shi da kuma yada shi. Babu wani batun kakabe ga jama’a ta karfi, kamar yadda addinai kanyi.

5. Fadin duniya dai a baya-bayan nan, kowa na waiga wa Insaniyya ne, muddin ya farga da yadda addinai masu kakaba kansu a rayuwar jama’u. ke kaka-gida, a rayuwar jama’a. Kishin Dan Adam da tausayi da kyautayi, da kirki, su suka haifar da Insaniyya, ko kuma ma a ce, su suka farfado da ita, bayan addinai sun kore ta tun daga yarintar mu.

Addinai sun tsayar da zamunna chak, bisa burin sai lallai an zauna a kan yadda suka dauka duniya take, a bisa tsohon tunani maras kan gado, na tun zamanunnuka da suka shude, lokacin da ba ilimi, ba fahimta, babu kuma cikakkun bayanai kan ya rayuwa take.

Insaniyya ta dogara ne da ilimi, da bincike da ma waiwaye don gyara.

6. Insaniyya na daraja fikira, ta tunani, kere-kere, sana’antawa da ma sabon tunani. Haka ma al’adu, duk abubuwa ne da jama’ar duniya a insaniyyance suka yarda suna da amfani.

Yaruka, zube, adabi, wake-wake, nishadi, kade-kade duk al’adu ne na bil’adama da suke iyar da labarin zaman rayuwar mu a doron kasa.

7. Insaniyya dai, zabi ne na rayuwa, wadda ke kokarin samar wa da bil-adama, rayuwa ta farin ciki, cike da wadata, ta zuci da ta waje, rayuwa Ta tarbiyya wadda babu cin zali ko karfa-karfa kan kowa a cikinta, tare da warware wa juna matsalolin yau da kullum.

Insaniyya dai, na iya zamewa kowa in yaso, hanyar rayuwa a koina a fadin duniya da kewaye, a kuma kowanne zamani.

Kokarinmu shine, nuna wa jama’a cikin sauki, yadda zamantakewa mai dorewa take. Da ma irin yadda zasu bi rayuwa bisa turba ta son juna. Ta hanyar amfani da yantaccen tunani wanda ba’a takure shi da ban-tsoro na chamfin addinai ba, sai zabin aiki da ilimi, zama lafiyar duniya bisa tausayi.

Muna da yakinin cewa, ta haka ne zamu iya warware wa juna matsalolin bilAdama.

Muna kira ne ga duk wadanda suke kan irin wannan tunani, dasu su hado kai domin wannan kokari”.

- Taron duniya na kungiyar masu rayuwar Insaniyya Wato IHEU a shekarar 2002 a birnin Amsterdam.

Translated By:

Mubarak Bala,
Trustee, Nigeria Humanists Association, and Northern Nigeria Humanists Association.Comments:


Please email comments to brighterbrainsinstitute@gmail.com